Gwamnatin Kano ta Fara Rabon Dabino da Kasar Saudia ta Bayar Dan Rabawa Al'umma.

Gwamnatin Kano ta Fara Rabon Dabino da Kasar Saudia ta Bayar Dan Rabawa Al'umma.

 



Karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano ya mikawa gwamnatin Jihar Kano Tan 50 na dabino a wani bangare na ayyukan agaji duk shekara.

Shirin wanda cibiyar ba da agajin jin kai da taimako  ta Sarki Salman ta dauki nauyi na da nufin tallafawa iyalai masu rauni a fadin Najeriya da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

A yayin taron, babban jami’in offishin  a Najeriya Khalil Admawy, ya tabbatar da kudirin masarautar Saudiyya kan ayyukan jin kai.

Ya bayyana matukar godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdelaziz da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa goyon bayan da suke ba wa musulmi da al'ummomi a duniya baki daya.

Ya kuma jaddada cewa Saudiyya na nan daram a kan kudurin da ta dauka na samar da hadin kan Musulunci da kuma samar da agaji ga masu bukata.

Ya kuma bayyana cewa rabon dabino na bana ya hada da tan 50 na dabino a Abuja da aka yi a makon jiya da kuma tan 50 a Kano da wasu jihohin arewacin Najeriya wadanda ake ci gaba da shirye-shiryen kai musu.

Ya kara da cewa, wannan shiri na wakiltar babbar manufar Masarautar ta daukaka al’ummar Musulmi, da rage radadin rayuwa, da inganta hadin kai.


Source: Arewa Radio

Published by: Abubakar D. Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post