Yadda Babangida Su Kayi Da Dimka a Shekarar 1976

Yadda Babangida Su Kayi Da Dimka a Shekarar 1976






Sunan Janar Ibrahim Babangida ya fara fitowa a duniya, tun a ranar 13 Ga Fabrairu, 1976, ranar da abokin sa Kanar Bukar Suka Dimka ya kashe Shugaban Kasa na mulkin soja a lokacin, Janar Murtala Ramat Muhammad wajen karfe 8:30 na safiyar ranar.

Bayan da Dimka ya kashe Murtala, sai ya zarce gidan rediyon tarayya da ke Lagos, in da ya fara yin sanarwa. Sai dai kuma ya na cikin yi wa ‘yan Najeriya jawabin ne, sai Janar dan Danjuma ya umarci Babangida yaje gidan Radiyo ya kamo Dimka ko ta halin ka'ka. Babangida ya darkaki gidan radiyon ya na mai jagorantar rundunar sojoji da motocin sulke da aka tura don ta murkushe Dimka.

IBB ya shiga gidan Rediyon ne domin ya shawo kan Dimka da ya yi watsi da yunkurinsa na kwace mulki. Maimakon IBB ya yi amfani da Karfi sojoji kamar yadda aka bashi umarni sai ya zabi hanyar lallashi.

Juyin mulkin ya ci tura," kamar yadda ya shaida wa Dimka. "Dole ka mika wuya." Sai Dimka ya yi barazanar zai harbe shi, sai IBB yayi murmushi ya shaida wa Dimka kashe ni, in ka kashe ni nasan matata da ‘ya’yana ba za su sha wahala a karkashin kulawar ka ba. Sai Dimka zuciyarsa ta karaya kuma ya nemi a yi masa afuwa idan an kafa sabuwar gwamnati, in da yake cewa Babangida, zai taka muhimmiyar rawa.

IBB ya fita da nufin zuwa neman izinin tattauna batun neman Sulhu daga Dimka. IBB ya koma wurin Danjuma wanda ya fusata da wannan bukata da ya kawo. Danjuma Ya dakawa IBB tsawa da cewa, “Ban nemi kaje don sulhu ba! a lokacin da IBB ya dawo gidan rediyon Najeriya cikin Sauri Kafin ya Karasa Dimka ya tsere.

Daga baya an kama Dimka da Taimakon wata karuwa a gabashin Najeriya a lokacin da yake kokarin tserewa zuwa Kamaru. A ranar 15 ga watan Mayu 1976, aka Harbe shi a bainar jama'a saboda laifin cin amanar kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post