Saudiyya ta Bada umarnin fara duban Watan Ramadan

Saudiyya ta Bada umarnin fara duban Watan Ramadan


 

Kotun Koli ta Saudiyya a hukumance ta yi kira da mazauna kasar da su duba jinjirin watan Ramadan mai alfarma a daren Juma’a, 28 ga Fabrairu 2025, wanda ya yi da 29 ga Sha’aban 1446 AH.

Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin Haramain Sharifain.

Duk wanda ya ga jinjirin watan da idonsa ko kuma ta hanyar amfani da na'urar hangen nesa (binoculars) ya sanar da kotu mafi kusa da shi domin bada shaidarsa, ko ya tuntuɓi cibiyar da ke kusa da shi domin taimaka masa wajen isa kotun mafi kusa.

Post a Comment

Previous Post Next Post