Janar Yohanna Kure Rtd, wanda ya jagoranci dakarun soji wajen murkushe Marwa Maitatsine da jama'arsa a Kano a shekarar 1980 da kuma a Yola a shekarar 1982, ya mutu a jihar Kaduna, yana dan shekaru 84 a Duniya.
Yohanna Yerima Kure (mai ritaya), tsohon Janar kuma kwamandan bataliyar ta 82 na sojojin Najeriya a Enugu, da kuma ta 2 a Ibadan,
Kure, wanda kuma shi ne Daraktan ayyuka na musamman da tsare-tsare na sojoji, ya mutu ne a Kaduna bayan ya sha fama da jinya.
Ya jagoranci Sojoji wajen murkushe kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta Maitatsine a Kano a 1980 da Yola a 1982.
Ya mutu ya bar matarsa, ‘yan’uwansa, ‘ya’ya da dama da al’umma jikoki.
Za a yi jana’izar janar Kure a ranar 1 ga Disamba, 2023 a mahaifarsa, Kurmin Musa, karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
Source: Daily Nigerian Hausa