Dr. Engr Hadi Usman, shine dattijo dan shekara 70 wanda bai taba zuwa makarantar Boko ba, kuma ya kirkiri na'urar sadarwa ta Rediyo, Injin Vespa, jirgi mai saukar angulo, wayar salula, da sauran su.
Dr. Engr Hadi, ya dirka a jami'ar jihar Gombe, inda ya gabatar da wasu fasahohin kirkira da yayi, a yayin da ake bikin yaye dalibai 'yan zangon karatu na, 11th, 12th da 13th a jami'ar ta Gombe.
A karshe jami'ar ta karrama shi da lambar girmamawa ta Dr. duk da kasancewar bai taba shiga aji ba.
A baya bayan nan ya kirkiri wani injin bada hasken wutar lantarki wanda baya bukatar amfani da Man fetur domin bada hasken wutar lantarki, haka ma ya kirkiri Murhun Girki da yake amfani da ruwa domin amfani dashi wajen yin girki.
Dr. Bai taba halartar makarantar boko ba, amma dai mahaddacin Al-qur'ani mai tsarki ne, kuma dan asalin jihar Gombe, yana zaune a anguwan Jekadafari.
Wannan shine 'Skills Rather than Just Degrees' kwafin littafin da malaminmu Sheikh Professor Isa Ali Pantami ya rubuta, gashi tun a yanzu muna ganin zahiri.
Reported by: Salisu Muhammad