AUREN GATA: Wani Bawan Allah yayi Alkawarin karawa da Katan din Indomie a Garar da Za'a Bawa Zawara Da 'Yan Mata Da Gwamnatin Kano Zata Aurar

AUREN GATA: Wani Bawan Allah yayi Alkawarin karawa da Katan din Indomie a Garar da Za'a Bawa Zawara Da 'Yan Mata Da Gwamnatin Kano Zata Aurar

 



Sheikh Muhammad Aminu Ibrahim ya kai ziyarar gani da ido yayin da shirye-shiryen auren Matasa da Zawarawa a Kano yayi Nisa. Kamar yadda kuke gani, ga Shehin Malamin nan kusa da buhunhunan shinkafar gara inda wani bawan Allah yayi alƙawarin ƙarawa da Indomie.

Kwamanda Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya yabawa shugaban Kungiyar kafintocin (Gandun Albasa General Furnitures Association) karkashin jagororin shugaban ta Alh Nafiu Nuhu Gandu bisa yanda suka jajirce wa wajen futar da gwamnati kunya akan aikin data basu.



Duba da kokarin da wan nan kungiya tayi hakan tasa Malam Aminu Daurawa ya nada shugaban ta jagoran kwamitin duba kayan gadajen da akayi a ragowar kasuwannin furnitures na jihar Kano.

Read more....... 

Read more.......

Watch video....... 

Wannan Aure dai shine aure mafi girma da aka taɓa yi a duk faɗin duniya kamar yadda Malam Daurawa ya shaida.




Wannan aure dai zai gudana ne ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Kano wanda Abba Kabir Yusuf zai ɗora akan inda Kwankwaso ya tsaya.


   #AURENZAWARAWA              #HISBA

Post a Comment

Previous Post Next Post