Shugaban Kasa Tinubu ya Raba Biliyan Biyar Ga Kowace Jiha Dake Nigeria

Shugaban Kasa Tinubu ya Raba Biliyan Biyar Ga Kowace Jiha Dake Nigeria

 



Gwamnatin Tarayyar Nijeriya karkashin shugaba Bola Tinubu ta bai wa kowacce jiha ta kasar da babban birninta Abuja naira biliyan biyar don rage radadin janye tallafin fetur

Ga bayanan abubuwan da za a yi da kudaden:

1. Kowace jiha zata sayi buhun shinkafa dubu dari,

2. Kowace jiha zata sayi buhun masara dubu arba'in

3. Kowace jiha zata sayi takin zamani

4. Za'a sayi motoci masu amfani da iskar gas.

5. Kashi 48% bashi ne jihohin zasu dinga biya a cikin wata 20

Wani Matashi Mai suna Hassan Kabir Asfakaf. Yayi fashin baki, yayi fashin baki akan wadannan kudade da shugaban ya bayar inda yake cewa.

Maigirma Shugaban Nigeria Tinubu ya bawa kowani Gwamna a Nigeria kudi Naira biliyan 5 domin su rabawa talakawan jihohinsu a matsayin rage radadin cire tallafin man fetur

Mun shaida Tinubu ya bawa Gwamnoni kudin, yanzu ya rage talakawa su sa ido wa Gwamnoninsu ko kudin zai iso zuwa garesu Sannan ayi ta addu'ah Allah Ya jefa tausayi da imani a cikin zukatan Gwamnoni su bawa talakawa hakkinsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post