A cikin satin da ya gabada har zuwa yanzu mutane suna tofa albarkacin bakinsu akan wannan shiri na MATA A YAU da talabijin din arewa24 tv ke gabatarwa inda cikin shirin daya daga cikin masu shirin ta kawo wani babban al’amari wanda sam bai dace ba tana yar musulmi amma ta kawo wannan zancen akan wai “miji ne zai saki Matarsa saboda bata gaishe shi” a nasu tunanin ya nuna cewa wannan sam bai dace ba kuma wai shirin na fadakar da mata zaman aure ne.
Sheikh lawan Abubakar Triumph yayi tsokaci akan wannan shiri da tashar keyi inda yake cewa.
“Yanzu akwai wani lalatacen shiri da akeyi a wata tasha wai “Mata A Yau” billahilazi idan anka cigaba da wannan shiri adadin zawarawa a kasar hausa zai karu kuma bincikenmu ya tabbatar wallahi da gayya anka kawo shi, duk wanda yake mu’amala da wannan gidan tv zai gayamaka shiri biyu sunka fi baiwa muhimmanci , shiri na farko shina wannan hiphop din zafafa goma 10.