Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce, tunda yanzu shi ne ke kula da lamurran jam'iyyar, to Kwankwaso zai iya sauya shekarsa. Ganduje ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da wasu kafafen yada labarai a cikin daren da ya gabata a jihar Kano, yana mai cewa,
Babu wanda zai ce Kwankwaso ba kwararren dan siyasa ba ne, akalla ya rike kujerar gwamna har sau biyu, koda yake a wani lokacin ya zama Ministan Tsaro duk da cewa, ba shi da masaniya kan tsaro kuma ya taba zama sanata duk da cewa, bai taba tsokaci ba har ya kammala zamansa a majalisa.
Ganduje ya kara da cewa, " Amma idan yana son sauya sheka zuwa APC, kofa a bude take, musamman a yanzu da wani daga jiharsa ya zama shugaban jam'liyyar, ba zai sha wahalar kamun kafa ba."
Lokacin da aka tambaye shi kan dalillin rashin sanya sunan Kwankwaso cikin jerin sunayen ministocin Tinubu, sai Ganduje ya ce, dama daga bakin Kwankwaso aka fara jin rade-radin, amma ba daga Tinubu ba
Da gaske ne shugaba Tinubu ya yi alkawarin gudanar da gwamnatin hadin-kai, kuma ya cika alkawarinsa . Nyesom Wike daga PDP, yanzu yana cikin wadanda ake son nadawa ministoci. Amma shi ( Kwankwaso), shi da kansa ne ya ce, za a nada shi, ba shugaban ba ne ya fadi haka" inji Ganduje.
Ganduje dai ya yi wa Kwankwaso mataimakin gwamnan jihar Kano har sau biyu tun daga shekarar 1999-2033 da kuma 2011 zuwa 2015, yayin da daga bisani suka samu rashin jituwa a tsakaninsu.
Source: RFI Hausa
Reported by: Abubakar D. Bature