Haɗin kan ‘yan Film a Masana'antar Kannywood wani jigo ne ga Cigaban masana’antar da kuma kima da martaba a gare su | Hajiya Zulai Bebeji

Haɗin kan ‘yan Film a Masana'antar Kannywood wani jigo ne ga Cigaban masana’antar da kuma kima da martaba a gare su | Hajiya Zulai Bebeji

 



Wannan kalamin ya fito ne daga bakin shugabar kungiyar Matanmu A yau Organization ta Kannywood Artists Hajiya Zulai Bebeji a lokacin da take yi wa manema labarai bayani a game da manufofin kungiyarta ta in da ta ke cewa.

“Mu dai Mata ‘yan fim mun yi ƙoƙarin samar da wannan kungiyar ne tun kusan shekaru biyu da suka wuce in da muka yi ta fadi tashin ganin kungiyar ta zauna da gindinta don ta zama wata inuwa ta haɗin kai da kuma taimakon juna a tsakanin mu, kuma Alhamdulillah kamar yadda abubuwa su ke tafiya a yanzu mun fara ganin hasken tafiyar.”

Ta ci gaba da cewa ” Da farko mun yi tunanin tafiyar da kungiyar iyakarmu mu Mata, amma daga baya sai muka faɗaɗa muka shigo da maza saboda duk wata harkar da mata za su yi sai maza sun shigo za a samu abin da a ke so na ci gaba, don haka ne muka shigo da maza a cikin tafiyar, amma dai mata sun fi yawa.”

Da muka yi mata tambaya a kan ko a yanzu me kungiyar ta fi mayar da hankali a kan sa kuwa cewa ta yi.

“To muna mayar da hankali wajen wayar da kan “yan fim wajen kula da muhimmancin sana’ar su don su kare mutuncin su da kuma masana’antar don haka ne ma mu ke haɗa taruka mu na gayyato manyan mutune su na yi mana jawabi, sannan mu na kai ziyara ga shugabanni da kuma ‘yan siyasa domin gabatar da kan mu da kuma manufar tafiyar mu.

Sannan ta cigaba da cewa suna ƙoƙarin samar wa kungiya ayyuka a wajen kamfanoni da kuma ‘yan siyasa, kuma duk wata jaruma da take cikin su, suna ƙoƙarin samar mata da aiki a wajen manyan Furodusoshin su na kannywood.”

A game da yadda a ke kallon kungiyar kamar ta tsofaffin ‘yan fim musamman Mata kuwa cewa ta yi.

“Kungiyar mu ta kowa da kowa ce yara da manya don haka ne ma a ke yi wa tafiyar ta mu kamar ta manyan ‘yan fim. To mu mu na yi ne da kowa don ba mu ware ba, kowa ya shigo namu ne da dan wasan daɓe da duk wani Wanda yake da harkar sana’a a cikin masana’antar fim don haka kungiyar mu ta kawa ce in dai ya na cikin kannywood”. Inji Hajiya Zulai Bebeji.

Kungiyar da ta haɗa ‘yan fim irin su Hajiya Zulai Bebeji da Bilki Madaki da Maryam Muhammad Maryam CTV da Hamza Adamu Indabawa da Nura MC da Hajiya Halima Sagir.

Sauran sun haɗa da Rukayya Sharaɗa da Zainab Isa Jalingo da Hajiya Maimuna da Hajiya Aisha da Hajiya Sakina da Bilkisu Muhammad da Firdausi KJB da Aisha Muhammad tare da Aisha KT da Hajiya Hauwa Ja’en Rahama Mil9 da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post