Gwamnatin Kano ta Rage Kashi 50 na kuɗin Karatu na Manyan makarantun Gaba da Sakandire

Gwamnatin Kano ta Rage Kashi 50 na kuɗin Karatu na Manyan makarantun Gaba da Sakandire

 



Gwamnatin jihar Kano Karkashin Jagorancin mai girma H. E Abba Kabir Yusuf ta sanar da zaftare kashi 50 cikin 100 na kuɗin makaranta ga ɗalibai ƴan asalin jihar da ke yin karatu a makarantun gaba da sakandare.

Kwamishinan Ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Kofar-Mata ne ya sanar da haka a jiya Litinin, yayin da ya ke ganawa da manema labarai.

gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin ta ragewa iyaye radaɗin biyan kuɗin makaranta, sakamakon matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta da cire tallafin man fetur ya haddasa.

Ya bayyana cewa ragin kuɗin makarantar ya shafi ɗaukacin ɗalibai da ke karatu a manyan makarantu mallakar gwamnatin jihar Kano, a zangon karatu na 2023/2024.

Makarantun, a cewar sa, su ne Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aiko Ɗangote Wudil (ADUST), Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK), da Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi.

Ragowar sun haɗa da, Kwalejin kimiyya fasaha ta jihar Kano (Polytechnic), da Kwalejin nazarin ilimin shari’a (Legal), Kwalejin harkokin noma ta Audu Bako Dambatta, Kwalejin share fagen shiga jami’a ta Rabiu Musa Kwankwaso da ke Tudun Wada, da kuma Kwalejin Ilimi ta jihar Kano.

Wannan ragi ya Biyo bayan, ɗaukar  mataki  da kokarin gwamnatin jihar Kano na haɓaka harkokin ilimi.

Post a Comment

Previous Post Next Post