Manhajar Threads ta samu rijistar mutane miliyan 100 a kwanaki 4 da ƙaddamar da ita

Manhajar Threads ta samu rijistar mutane miliyan 100 a kwanaki 4 da ƙaddamar da ita

 



Sama da mutane  miliyan ɗari sun yi rajista da manhajar Threads cikin kwanaki huɗu da ƙaddamar da ita. A ranar 6 ga Yuli, Mark Zuckerberg, wanda ya kafa Meta, kamfanin da ke ɗauke da Facebook da Instagram, da WhatsApp, ya kaddamar da zauren domin yiwa abokin hamayyarsa, Elon Musk na Twitter kishiya.

Kaddamar da manhajar na zuwa ne kwanaki bayan da Musk ya sanar da cewa an sanya dokar wucin-gadi kan adadin sakonnin da masu amfani  za su iya karantawa kullum a shafin Twitter.

Ya ce masu amfani da aka tantance za su sami damar yin rubutu na kalmomi 6,000 a kullum, yayin da ba a tantance ba kuma za a bar sabbin masu amfani da su karanta 600 da 300, bi da bi.


Bayan kaddamar da Threads, Twitter ya yi barazana ga Zuckerberg da wata shari'a kan "lalata da sirrin kasuwancinsa ba bisa ka'ida ba."

A cikin takardar ƙorafi Alex Spiro, lauyan Twitter, ya bayyana Threads a matsayin "copycat" kuma ya ce Meta ya dauki hayar tsofaffin ma'aikatan Twitter da yawa wadanda "suna da kuma ci gaba da samun damar yin amfani da bayanan sirri na Twitter

Post a Comment

Previous Post Next Post