Juyin Mulki: Halin da ake ciki a Niger Bayan Juyin Mulki

Juyin Mulki: Halin da ake ciki a Niger Bayan Juyin Mulki

 



Yanzu dai ta tabbata anyi juyin mulki a Niger Da misalin karfe 12:30 na dare ne wasu sojoji kalilan suka fito gidan Talabijin din kasar suka tabbatar da juyin mulkin da sukayi .

Kakakin Sojojin kasar Manjo Ahmadou Abdulrahamane ne ya sanar da hakan
Ya ce daga yanzu sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin kasar Sannan Kuma sun rufe duk iyakokin kasar baki daya zuwa yanzu dai babu wani labari game da halin da Bazoum Mohamed ke ciki

Amma sojojin sun bayar da sanarwar kwace mulki daga hannunsa Sojojin sun ce sunyi juyin mulkin ne saboda halin da Niger take ciki na tabarbatewar tsaro da tattalin arziki

Juyin mulkin ya biyo bayan zargin aikata laifula da faransa ke wa shugaba bazoum kamar haka.



1. Ya ki yarda kasar ta ci gaba da bautar da kasarsa kamar yadda ta saba.

2. Ya nu na a fili cewa  yana son kasarsa ta daina amfani da Saifa domin samawa kasar kudi mallakinta.

3. Kwanakin baya wajen buɗe matatar Man Fetur ɗin Dangote a Legas, ya yi jawabi da Hausa mai makon Faransanci, hakan ya janyo manyan yan bokon kasar na Nijar suke ƙalubalnatansa na karya dokokin ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post