Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naÉ—a tauraron Kannywood, Abba El-Mustapha a matsayin Sakataren Gudanarwa na hukumar tace fina-finai ta jihar Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da wannan naÉ—in a ranar Litinin.
Abba El-Mustapha wanda ake yi wa taken “Abba na Abba” saboda kusancinsa da gwamnan ya maye gurbin Alhaji Isma’ila Na’Abba Afakallah. An dai kafa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ne domin É—ora fina-finai da littattafan Hausa bisa tafarkin adddini da al’adar al’ummar Kano.
Sai dai hukumar ta yi ƙaurin suna wurin kama ƴan Kannywood musamman masu adawa da gwamnatocin dake mulki a jihar.
Tags:
News