Hukumar gudanarwar kamfanin A. A Rano Nigeria Limited ta musanta cewa tana sayar da man fetur a kan farashin N400 a kowace lita.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa jita-jitar cewa A.A. Rano na sayar da man fetur a kan kudi N400 ya yi ta yaÉ—u a shafukan sada zumunta daban-daban.
Sai dai kuma da ya ke mayar da martani ga wannan jita-jita, kamfanin, a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na sada zumunta, ya bayyana rahoton a matsayin yaudara.
Click to Apply for a Job Online
Mahukunta a AA Rano sun yi watsi da labaran karya da yaudara na sayar da man fetur a kan kudi N400 a wasu tashoshin da aka zaba.
"Ku yi watsi da wannan labarin na karya gaba dayansa," in ji sanarwar.