Marigayi Danmakwayon Kano Yusuf dan Muhammad Bashir dan Galadiman Kano Yusuf Maje-Garko dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo, A tarihin masarautar Kano, shi kadai ne dan Sarki da ya taba yin Hakimci a Gaya.
An haife shi a shekarar 1891 Miladiyya. Ya taso a hannun Sarkin Kano Abbas Maje-Nassarawa wanda kani ne ga kakansa wato Galadiman Kano Yusuf Maje-Garko. Ya yi karatun addini a makarantar 'ya'yan Sarki ta Kofar Kwaru a hannun wani malami mai suna Mallam Umaru wanda yake koyar da 'ya'yan Sarki a wancan lokacin.
Sun yi karatu a wannan makarantar tare da mutane irin su Ahamdu Abbasi (Wanda daga baya ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida) da Ahmadu Sufi da Sulaiman (Wanda ya zama Walin Kano). Haka kuma, tare da wannan abokai nasa suka yi karatu a unguwannin Jar-Kasa da Yola da Madabo duk a cikin birnin Kano, daga bisani kuma suka tafi kasashen Zazzau da Katsina da Maradi inda suka yi karatu a wajen malamai da dama.
Wannan ta sanya Mallam Yusufu ya zama cikakken malami, har ma ana yi masa kirari da "Mallam dan Mallam, maso zama da kai ya yi sallah," kuma yana daga cikin malaman da suka koyar da Marigayi Maimartaba Sarkin Kano Muhammad Sanusi I tun kafin ya zama Chiroman Kano.
A bangaren mukaman sarauta kuma, Mallam Yusufu ya rike mukamin Karamin Malamin Chiroman Kano Sanusi Hakimin Bichi inda yi yi aiki tare da daya daga cikin abokan nan nasa wanda suka yi karatu tare wato Mallam Ahmadu Sufi; wanda shi ne yake rike da mukamin Babban Malamin Hakimi a wancan lokacin.
Bayan rasuwar Mallam Ahmadu Sufi a shekarar 19231, sai aka ciyar da Mallam Yusufu gaba ya zama Babban Malamin Hakimin Bichi kuma Wazirin Chiroman Kano. A shekarar 1940, Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya nada Mallam Yusufu sarautar Dan makwayon Kano Hakimin Garki, daga nan aka yi masa canji zuwa Jahun a shekarar 1943, daga Jahun kuma aka mayar da shi Gaya inda ya yi hakimci tun daga shekarar 1949 har zuwa rasuwarsa a shekarar 1968.