Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Kyauta - CCB

Shanun Buhari Sun Ragu Saboda Kyauta - CCB

 



Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya miƙa takardar da ya cike da ke ƙunshe da bayanan kaddarorin da ya mallaka ga hukumar ɗa'ar ma'aikata CCB bisa tanadin shafi na shida na Kundin tsarin mulkin ƙasa.

 Hukumar ta CCB ta tabbatar da karÉ“ar fom din tsohon shugaban Æ™asar.
Takardar bayanan ta nuna cewa kaddarorinsa da za a iya sauyawa wuri ba su ƙaru ba - a gida da kuma wajen Najeriya.



Sannan bai buɗe wani sabon asusun banki ba, baya ga wanda yake da shi a bankin Union a Kaduna, Bayanan sun ƙara da cewa, tsohon Shugaban bai karɓi bashi ba kuma adadin shanunsa sun ragu saboda ya bayar da wasu kyauta cikin shekara huɗu da ta gabata.


      #LABARAI                    #BUHARI

Post a Comment

Previous Post Next Post