Tsohon ministan yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed ya samu sabon aiki da wani kamfanin ayyukan kamun ƙafa na ƙasa-da ƙasa, na Ballard Partners. A wani sakon Tuwita da kamfanin ya wallafa ya ce ya naɗa Lai Mohammed a matsayin jami'in gudanarwa.
Sanarwar ta ce kamfanin na Ballard Partners wanda ke ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ke kyautata alaƙa tsakanin ɓangarorin gwamnati a Amurka, ya buɗe reshensa na farko a nahiyar Afirka a Abuja babban birnin Najeriya. Shugaban kamfanin Brian Ballard ya ce kamfanin ya bai wa Lai Mohammed aikin ne kasancewar yana ɗaya daga cikin mutanen da ake ganin kimarsu a Najeriya.
Jaridar Punch a Najeriyar ta ambato Lai Mohammed na bayyana jin daɗinsa na kasancewa ɗaya daga cikin ma'aikatan kamfanin Ballard Partners mai kyakkyawan tarihi a ayyukasa a faɗin duniya.
“Na ji dadin fara aiki da kamfanin Ballard Partners tare da buɗe ofishinsa a na farko a Afirka'', in ji Lai Mohammde. Lai Mohammed dai ya shafe shekara takwas a matsayin ministan yaɗa labarai a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammdu Buhari.