Yadda Ake Samun Kudi Da Facebook Stars a Professional Mode ko Page

Yadda Ake Samun Kudi Da Facebook Stars a Professional Mode ko Page

 



Facebook Stars wani tsari ne da facebook ke baiwa mutun damar samun kudi daga wajen followers dinsa ta hanyar posting dinda yake. Mabiyansa ko "Followers" dinsa zasu iya siyan "Stars" su turamasa a duk wani posting dinda akwai damar hakan ko ince anyi Enabling din Stars din. Posting din zai iya zama Video Post, Hoto, text dama ko wane iri harma da live video. Ga kowane Star da mutun yasamu facebook zai biyashi $0.01 USD dai dai da 4.41 a Naira.

Idan yazama kai mai yawan posting video da Reels ko posting haka, Facebook zai iya sakama Facebook Stars automatically basai kayi apply ba, idan kuma ba'a saka maka ba sai kayi apply. Sai dai wannan tsarin ba kowa Facebook ke baiwa ba sai wanda yacika ka'idar samun shiga tsarin, basai mai Page kadai ba Har wanda ke professional mode na iya samun damar shiga.

Daya daga cikin ka'idojin shiga wanna tsarin ga masu professional mode shine dole mutun yazamto yanada followers wanda bai gaza dubu ba (1000 followers) har tsawon kwanaki 60. Yana da kyau kafin mutun yayi apply ya tabbatar yacika ka'idojin, domin dubawa ko mutum yacika ka'idojin sai abi wannan hanyar.


Ga masu Professional Mode:

1. Da farko mutun yaje profile dinsa sai ya danna wajen digo guda ukun domin yakai shi dashboard dinsa.
2. Daga nan yadanna "Tools to Try" daga nan "Stars" don ganin ko ancika ka'idar.

Ga masu Pages: 

1. Da farko mutun yaje Creator Studio ta wannan link din 👇👇👇

 https://business.facebook.com/creatorstudio/home

2. Daga nan sai adanna "Monetization" dake gefen hagu. Ananne za'aga ko ancika ka'idar.
Idan mutun yacika ka'idojin ga yadda ake setawa ko ince Apply

Karin bayani:

1. Da farko mutun zaije inda "Tools to Try" yake, sai ya danna "Stars"

2. Yayi accepting "Terms and Condition" tun daga nan mutun zai fara ganin Stars din sun fara bayyana a post dinsa, sai dai mutun b azai fara samun earning dinsa ba har sai ya seta Payment account dinsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post