Rikicin Sudan: Turkiyya za ta ɗauke ofishin jakadancinta daga Khartoum zuwa Port Sudan

Rikicin Sudan: Turkiyya za ta ɗauke ofishin jakadancinta daga Khartoum zuwa Port Sudan

 



Turkiyya ta amince da sauya wa ofishin jakadancinta da ke Sudan matsuguni daga birnin Kahrtoum zuwa Port Sudan, bayan da aka harbi motar jakandanta da bindiga, Babu dai wanda ya jikkata a harin. Birnin Khartoum ya kasance filin daga a yaƙin da ake yi tsakanin dakarun sojin ƙasar da rundunar RSF.

Tun farkon fara yaƙin ne dai ƙasshen duniya da dama suka yi ta ƙwashe jami'an diplomasiyyarsu tare da rufe ofisohin jakadancinsu a birnin Khartoum. To amma Turkiya wadda babbar ƙawar Sudan ce ta ci gaba da barin ofishin jakadancin nata a buɗe.


To sai dai bayan harin bindiga da aka kai wa motar jakadan nata ta fara tunani sakewa ofishin matsuguni. Duka ɓangarorin sojin ƙasar da rundunar RSF sun zargi juna da kai wa motar jakadan Turkiyyar hari.

Yayin da suka amince da tattaunawar sulhu a Saudiyya domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar. Ana sa ran tattaunawar za ta kawo sauƙi ga fararen sama da miliyan bakwai da suka maƙale a gidajensu a birnin.



Post a Comment

Previous Post Next Post