Zababben shugaban kasa, Sen. Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ma’aikatan Najeriya da albashi mai kyau tare da kula da hakkin su da bunÆ™asa tattalin arzikin su, Ya ba da wannan tabbacin ne a yau Litinin a Abuja a sakon sa na goyon baya ga ma’aikatan Najeriya a bikin ranar ma’aikata ta duniya ta 2023.
Ya kara da cewa ma’aikata a kasar nan za su samu albashi ingantacce da za su samu rayuwa mai kyau da kuma wadata iyalansu a karkashin shugabancinsa.
Tsohon gwamnan jihar Legas É—in ya kuma tabbatar wa ma’aikatan Najeriya cewa shi abin dogara ne kuma abokin aiki a fafutukar tabbatar da adalci a zamantakewa da tattalin arziki ga daukacin Æ´an Nijeriya.
Tags:
News