Shugaban Az-zaman Mal. Bukhari Alhawari ne fitar da sanarwa a shafinsa na facebook inda ya fara da cewa.
Alhamdulillah, Alhamdulillah.
A cikin Ni'imar Allah da Falalar sa, tun bayan kafa wannan Cibiya mai Albarka a ƙarshen watan August 31 2022. Ta kuma fara ayyukan ta a watan September 2022. Mun samu Nasarori kamar haka;
1. Wanzuwar wannan cibiya mai albarka tun daga wannan lokacin har zuwa yanzu ba tare da rushewa ba.
2. Samar da (Az-zaman Delivery Services) domin samawa wannan cibiya kuÉ—in shiga.
3. Samar da Az-zaman Business Centre. Inda muke harkar Pos, don samar da kuÉ—in shiga.
4. Nasarar Kammala rubuta littafi biyu, wanda Director na wannan cibiya yayi a ƙarƙashin ta (Bukhari Alhawari) kamar haka:
• SaÆ™aƙƙen Al'ajabi daga Sihirin Tunani.
• Kalmomi Dubu da Daya game da Addini da rayuwa.
Abunda ya rage shi ne; a buga su. Da yarda Allah.
5. Gabatar da Kacici-kacici a cikin watan Ramadan, hadi da ba da muhimman kyaututtuka ga waÉ—anda suka yi nasara, domin karfafa musu guiwa game da ilimin addini.
6. Laccoci da aka gabatar kamar haka;
• ÆŠan uwan na Matashi. Daga ta É—aya zuwa ta bakwai.
• Lissafin dake cikin rayuwa. Daga ta É—aya zuwa ta biyu.
7. Seminar ta Rana ÆŠaya, Mai taken; Bakandamiyar Ya'ya Mata. Wadda aka yiwa iyaye Mata da kuma Yammata.
8. Shirywa, gabatarwa hadi da É—aukar nauyin gudanar da Ramadan Tafsir.
Alhamdulillah. Waɗannan sune Muhimman Nasarori da muka cimma guda takwas a wata takwas. Muna rokon Allah ya ba mu damar samun Nasarori cikin ayyukan da muka dosa a gaba. Kuma addu'ar ku ta Alkhairi ga wannan cibiya na da matuƙar muhimmanci. Allah ya taimaki musulunci da musulmi baki ɗaya.