Na yafe wa Buhari bisa Maida Nijeriya baya da ya yi - Ortom

Na yafe wa Buhari bisa Maida Nijeriya baya da ya yi - Ortom

 



Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta maida Najeriya daga sama zuwa kasa, amma ya yafewa shugaban kasar, Ortom, wanda zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a jiya Laraba.

Da ya ke bada hujja daga littafin Bible, ya ce: “Idan ba kwa yafiya, to hakan yana nufin Allah ma ba zai gafarta muku ba. A matsayina na dalibin Littafi Mai Tsarki kuma a matsayina na Kirista na gari, na gafarta wa shugaban kasa Muhammadu Buhari.


Ortom ya kuma bayyana fatansa na samun kyakkyawan shugabanci daga gwamnatin zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.
"Muna fatan gwamnati mai zuwa za ta ba da tallafi, taimako, tsaro, bunkasa tattalin arziki, da zaman lafiya ga jama'armu,

Sai dai ya shawarci Buhari da kada ya fice daga Najeriya, amma ya koma ya yi aiki da gwamnatin Tinubu domin daga likkafar kasar daga kasa zuwa sama Ba ya bukatar ya je Jamhuriyar Nijar. Ya zauna a nan (a Najeriya) tare da mu. Mu yi aiki da gwamnati mai zuwa kuma da yardar Allah za mu tashi daga kasa zuwa sama, inji ortom.


      #LABARAI                   #SIYASA

Post a Comment

Previous Post Next Post