Jarumin fim din Daɗin Kowa, Kawu Mala ya Rasu

Jarumin fim din Daɗin Kowa, Kawu Mala ya Rasu

 



Fitaccen jarumin wasan kwaikwayo mai dogon zango, Dadin Kowa, da ake nunawa a tashar Arewa24,  Aminu Muhammad wanda aka fi sani da Kawu Mala ya rasu.

Daily Trust ta rawaito cewa jarumin ya rasu ne da yammacin jiya Lahadi, bayan ya sha fama da ciwon zuciya na wasu shekaru.  Mala, wanda ya kwashe sama da shekaru 20 ya na wasan kwaikwayo, ya shahara sosai a cikin shirin Dadin Kowa TV inda ya taka rawar gani.

Jarumin ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya sama da 10.  An yi jana’izar marigayin a safiyar  Litinin data gabata a makabartar Haye da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.



Daya daga cikin abokan sana'ar sa, Murtala Karabiti, ya bayyana rasuwar Mala a matsayin babban rashi da ya haifar da babban gibi a masana’antar, inda ya kara da cewa har abada za a rika tuna da marigayin a matsayin wanda ya yi iya bakin kokarinsa wajen bunkasa harkar fim a arewacin Najeriya.

“Likita, kamar yadda muke kiransa, abokin kowa ne, kuma dan’uwa ne ga yawancinmu, na san shi sama da shekaru 20 kuma duk tsawon wadannan shekarun, ban taba jin wani mummunan magana game da shi ba. Ya riga ya  tafi, namu shi ne mu yi masa addu’ar samun Rahama.


       #TA'AZIYYA              #LABARAI

Post a Comment

Previous Post Next Post