Dan Wasan Kwalon Kafa Saka ya sanya hannu a Sabuwar kwantaragi mai tsayi a Arsenal

Dan Wasan Kwalon Kafa Saka ya sanya hannu a Sabuwar kwantaragi mai tsayi a Arsenal


Bukayo Saka ya rattaba hannu akan yarjejeniyar mai tsawo da zai ci gaba da taka leda a Arsenal. Dan wasan tawagar Ingila, ya ci kwallo 14 a Gunners a kakar nan da ake bankwana da ita, ya kuma bayar da 11 aka zura a raga.

Mai shekara 21 ya yi karawa 178 a kungiyar Emirates, ya kuma buga wa Arsenal dukkan wasannin Premier League a kaka biyu.
Tun farko kwantiragin Saka za ta karkare a Arsenal a karshen kakar 2023-24.

Apply for Indian Scholarship 👇

Arsenal, wadda take ta biyu a teburin Premier League za ta karbi bakuncin Wolverhampton a wasan karshe na kakar bana.

    

Post a Comment

Previous Post Next Post