Kotun Majistiri mai lamba 69 da ke Kasuwar Sabon Gari a Kano ta soma sauraron ƙarar da Asiya Balaraba Ganduje ta kai tsohon mijinta. Balaraba Ganduje na zargin tsohon mijin na ta Inuwa Uba da shiga waje ba tare da izni ba, tare da cin zarafinta ta hanyar gwada ƙwanji da yi mata rauni.
Bayan da aka karanta masa waɗannan tuhume-tuhume, tsohon mijin ya musanta.
Daga nan lauyansa ya nemi a bada belinsa.
Mai shari'a Ishaq Abdu Aboki ya amince da ba da belin bisa sharaɗin Naira 50,000 da gabatar da nagartattun mutane biyu kowa da Naira 20,000.
Kotun ta sanya ranar 25 ga watan Mayun da muke ciki domin ci gaba da shari'ar.
Source: Fredom Radio Nigeria
Tags:
News