An Harbi Jirgin Turkiyya kan Hanyar sa ta Kwaso ƴan ƙasar a Sudan

An Harbi Jirgin Turkiyya kan Hanyar sa ta Kwaso ƴan ƙasar a Sudan

 


Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ta bayyana cewa an harbi wani jirgin sojin Turkiyya da ke aikin kwashe ƴan kasar Turkiyya daga Sudan da ke fama da rikici, Jirgin mai lamba C-130 na Turkiyya ya nufi sansanin jiragen sama na Wadi Seidna domin kwashe ƴan kasarsa da ke birnin Khartoum.

Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya ci karo da harbin kananan bindigogi, a cewar sanarwar da ma'aikatar tsaro ta Turkiyya ta fitar a ranar Juma'a. Sanarwar ta kara da cewa, a cewar TRTWorld jirgin ya sauka lafiya, kuma ba a samu wata matsala ba.


A yayin mayar da martani kan rahoton, sojojin Sudan sun zargi dakarun sa-kai na Rapid Support Forces, da harbin jirgin sojin na Turkiyya, Sai dai kuma  RSF din ta musanta cewa ta harbo jirgin inda ta nace cewa sojojin Sudan na yada karya.


Hanyar da zaka samu kudi online



Post a Comment

Previous Post Next Post