Gamayyar kungiyoyin goyon bayan Gwamna Ahmadu Fintiri sun yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC da ta sake gudanar da zaben gwamna cikin gaskiya da adalci, wanda aka shirya gudanar wa a ranar 15 ga watan Afrilu.
Abdulrahaman Bobboi, mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin ne ya yi wannan kiran yayin da ya ke gabatar da wasikar su ga Fintiri da INEC a Yola yau Laraba. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.
Sai dai kuma Bobboi ya ce jam’iyyar PDP ta samu tazarar kuri’u 30,000 a saman ƴar takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, wacce ta zo ta biyu a zaben. PDP na buƙatar karin kuri’u a lokacin sake zaben.
"Muna fatan samun nasara, saboda babban sakamakon da aka samu ya nuna cewa PDP ce ke kan gaba a zaben, saboda kyakkyawan jagoranci na Fintiri a cikin shekaru hudu da suka gabata. "Muna fatan samun nasara, saboda babban sakamakon da aka samu ya nuna cewa PDP ce ke kan gaba a zaben, saboda kyakkyawan jagoranci na Fintiri a cikin shekaru hudu da suka gabata.
“Saboda haka, muna kira ga INEC da ta sake gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci a wuraren da abin ya shafa,” inji shi. haka, muna kira ga INEC da ta sake gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci a wuraren da abin ya shafa,” inji shi.