Dikko Umar-Radda, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Katsina, ya ce gwamnatinsa za ta rungumi fasahar zamani wajen yaki da rashin tsaro a jihar. Umar-Radda ya bayyana haka ne a jiya Juma’a a fadar shugaban kasa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Katsina dai na fama da matsalar rashin tsaro a ƴan shekarun nan.
A bara ne aka kashe manoma 12 a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa al’umma hari. Umar-Radda ya ce dole ne a samar da tsaro a jihar domin ayyukan tattalin arziki da noma su bunkasa.
“Noma babban yanki ne na rayuwa ga mutanenmu. Dole ne mu samar da tsaro domin mutanenmu su yi noma. Za mu shigar da mazauna jihar tare da yin amfani da fasahar zamani wajen magance matsalolin tsaro a jihar ta mu, "in ji Radda.