Rikicin Sudan: Dalilan da Suka Janyo Yaki a Kasar Sudan

Rikicin Sudan: Dalilan da Suka Janyo Yaki a Kasar Sudan

 



Wannan rikici na kasar Sudan fadane tsakanin sojojin kasar Sudan da kuma sojojin dake adawa gwamnatin soji ta kasar, Wanda rikicin ya fara afkuwa a ranar 15 ga watan Afrilun wannan shekara da muke ciki yau Kwana bakwai kenan da fara wannan yaki.

Yakin ya barke ne a kasar musamman yankin Babban Birnin Kasar Khartoum da kuma yankin Darfur, Wanda rahotanni sun nuna daga fara yakin zuwa yau An rasa kimanin Rayukan Mutane 413 yayin da aka raunata akalla mutum 3,500.

Sojojin adawa da ake kira Rapid Support Forces (RSF)  Sunfara kai harehare a manyan Ma'aikatun gwamnati Karkashin Shugabancin  Mohamed Hamdan Dagalo Wanda yake jagorantar Sojin Adawa a kasar yayi ikirarin kwace iko a wasu Ma'aikatu na gwamnati, agefe guda kuma Shugaban Sojojin Kasar ta Sudan Wanda ke jagorantar Sojojin kasar Chief Abdel Fattah al-Burhan shima yayi wannan ikirarin.


Dukkan bangarorin biyu sunyi ikirarin Mallakar da yawa daga wasu Ma'aikatun gwamnati dake karkashin ikonsu, Wanda ya hada da Babbar headquarter sojojin kasar da kuma Gidan gwamnati da Babban filin sauka da tashin jirage na kasar.

Bangaren sojojin adawa suna samun goyan baya daga kasashen waje kamar Sojojin Kasar Libya da kuma Kasar Russia (Rasha). A yayin da  Sojojin Kasar Sudan suke da goyan bayan Kasar Egypt. A yanzu haka dai daliban Nigeriya suna cikin tsaka mai wuya, Kuma sunyi kira da Hukumomin Nigeriya dasu taimaka su zo su kwashesu a dawo dasu gida, musamman daliban da suke ayankin  Khartoum.

Post a Comment

Previous Post Next Post