Ma'anar Technology da Abinda ya Kunsa | Asua Daily Post

Ma'anar Technology da Abinda ya Kunsa | Asua Daily Post

 



Technology ko Technical shi ne abun da muke kira fasaha da Hausa. Wasu suna amfani da kalmar fasahar zamani don nuna abun da ake kira Digital Skill. Ita kalmar dijital tana nuna yadda na’ura take fassara abubuwa ta hanyar amfani da lambobin sufuli da kuma É—aya (1 & 0). Kada na cika ku da ruÉ—ani, abun da nake nufi da fasahar zamani a duk inda ta fito a rubutun nan in dai ban bayyana akasin haka ba to shi ne “Digital Skills”.

Canjawar duniya ko in ce ci gaban da ake samu ta fuskar fasaha a zamanance ya wajabta wa kowa koyon fasahar zamani a wannan Æ™arnin matuÆ™ar yana so ya rayu, rayuwa mai armashi. Babu inda fasaha ba ta shiga ba a gaba É—ayan fannonin rayuwa, tun daga kan ilimi, kasuwanci, tattalin arziÆ™i,sana’o’i, siyasa, noma da kiwo da dai sauran É“angarori na rayuwa.

Wannan ya sa yake da muhimmanci a matsayinka na saurayi kar ka bari a dama babu kai. Idan kai dattijo ne ko kaɗan wannan maganar ba ta nufin kar ka koya, amma kamar yadda yake a zahiriyya ta rayuwa, matashin zai fi ka buƙatar nutsawa cikin koyo.


Mene ne misalan fasahar zamani?
Ilimin tushe/farko/na dole kan na’ura mai Æ™waÆ™walwa, wato basics computer skills: su waÉ—annan sun tattara tun daga kan yadda ake kunna computer, amfani da keyboard (wato madannanta), amfani da mouse da softwares na amfanin yau da kullum kamar su word processors (ta rubutu), spreadsheet (ta lissafi), Browsers ta shiga yanar gizo, Media players na kallon bidiyo ko sauraren audio, ga su nan dai barkatai.

Ilimi kan yanar gizo da dandalin sada zumunta (Internet and social Media) Mutane da dama suna ganin daga sun mallaki yar Vivo dinsu shikenan sun zama ƙwararru a harkar yanar gizo. Ilimin yanar gizo yana da faɗi, tun daga kan inda za ka kutsa ka samo bayanan da kake nema ta hanyar amfani da kamar Google, Bing, Yahoo. Sanin matakan kariya na farmakin mugaye a yanar gizo har da ma iya amfani da dandalin sada zumunta a yadda ya dace.


Post a Comment

Previous Post Next Post