Azumin bana: Saudiya da Najeriya Azumi 29 Zasuyi a ƙa'ida ta Ganin Watan Saudiya Ranar Juma'a 21/04/2023 Itace Zata Yi Dai-Dai da 1 Ga Watan Shawwal

Azumin bana: Saudiya da Najeriya Azumi 29 Zasuyi a ƙa'ida ta Ganin Watan Saudiya Ranar Juma'a 21/04/2023 Itace Zata Yi Dai-Dai da 1 Ga Watan Shawwal



Ga kaɗan daga cikin da lilan da yasa hakan zai faru Daga Gwani Mai Ismi Foundation
Daga ɗaya 1 ga watan Almuharram na wannan shekara ta 1444, zuwa 29 ga watan Ramadan an sami kwana 265.

Samun haihuwar sabon jinjirin watan SHAUWAL a ƙa'ida ta ilimin falaki/hisabi, yana faruwa ne a duk duniya sau ɗaya sai dai lokutan sukun banbanta daga ƙasa zuwa ƙasa saboda nisan da ke tsakanin ƙasashe,

A Najeriya za'a sami haihuwar sabon jinjirin watan SHAUWAL ne, a ranar a gobe Alhamis in Allah ya kaimu, 20/04/2023 wacce ta yi dai-dai da 29/09/1444, da Misalin ƙarfe 5:12 na safe (AM) a agogon Najeriya (GMT+1)  A Lokacin da RANA da WATA sun yi, conjunction/Muƙarana a cikin Burujin Himlu  ( حمل) akan digiri/daraja 29° sannan a cikin munzilar SURAYYA, (ثريا)


Daga samun haihuwar sabon jinjirin watan SHAUWAL zuwa lokacin da rana zata faɗi a Najeriya aƙallah an sami awa 13 da minti 33 wanda ya yi dai-dai da digiri/daraja 14°
Bayan faɗuwar rana da minti 20 wata zai faɗi a Najeriya,

A ƙasar saudiya a birnin Makka, a gobe Alhamis idan Allah ya kaimu, 20/04/2023, wacce ta yi, dai-dai da, 29/09/1444, za'a sami sabon jinjirin watan SHAUWAL ne, da misalin ƙarfe 7:12 na safe (AM) lokacin da wata suka yi, conjunction/muƙarana, lokacin ne, aka sami haihuwar sabon jinjirin watan SHAUWAL, abirnin Makka,

Daga lokacin da aka sami haihuwar sabon jinjirin watan SHAUWAL a birnin Makka na ƙasar Saudiya, zuwa lokacin da rana zata faɗi an sami awa 11 da minti 29 saboda rana zata faɗi a birnin Makka na ƙasar saudiya da misalin ƙarfe 6:41 na yamma (PM)

Sannan daga lokacin da rana ta faɗi a birnin Makka na ƙasar Saudiya zuwa lokacin da wata zai faɗi minti 24 za asamu, saboda WATA zai faɗi da Misalin ƙarfe 7:05 na dare (PM)


Post a Comment

Previous Post Next Post