Al'ajabi: Kabilar da Suke Shan Fitsarin Saniya Kuma Suyi Wanka Dashi

Al'ajabi: Kabilar da Suke Shan Fitsarin Saniya Kuma Suyi Wanka Dashi

 


Kabilu kala kala ne haka ma al'adun da ake gabatarwa cikin kowacce kabila sunada yawa sosai. Idan mutum yana rayuwa a bayan kasa zai rika gamuwa da abubuwan mamaki da al'ajabi na ban mamaki wanda ke rikitar da tunani daken faruwa a cikin wannan duniyar.

Wasu abubuwan da suke ko kadan bashi da wani kyau ko birgewa, amma duk da haka babu ruwansu hakan suke gabatarwa. Yau cikin shirin namu muna tafe muku da labarin wata kabila da suke shan fitsarin saniya kuma suyi wanka dashi.

Kabilar Mundari dake Juba can kudancin sudan suke wanka ko kuma su sha fitsarin saniya a matsayin magani wasu kuma suna amfani dashi wajen wanke gashin kansu domin ya kara kyau. A sauran kasashe kamar Nigeria su mutane suna amfani da kashin shanu da kuma fitsarin su a matsayin taki a gonakin su.


Amma su kabilar Mundari suna matukar girmama fitsarin saniya domin kuwa har wanka suke dashi ko kuma su wanke kansu dashi domin a cewarsu yana maganin cututtuka. Dan haka koda yaushe idanun mutane yana kan saniyoyin dake garin daga sunga sun fara fitsari zasu zo suna tara suna wanke fuskarsu dashi kuma suna sha.

Post a Comment

Previous Post Next Post