Na fadi zabe ne saboda tambarin jam'iyya ta ya yi dishi-dishi - Ƴar takarar Sanata ta NNPP

Na fadi zabe ne saboda tambarin jam'iyya ta ya yi dishi-dishi - Ƴar takarar Sanata ta NNPP



Helen Mbakwe, ƴar takarar jam’iyyar Sanata ta New Nigeria People’s Party, NNPP, ta ce ta sha kaye a zaben Sanata ne saboda tambarin jam’iyyar ta ya yi dishi-dishi a kan takardar dangwala kuri'a. Mbakwe, wacce ta tsaya takarar kujerar Sanatan Anambra ta Tsakiya, ta danganta rashin samun nasarar kujerar ne da rashin fayyace tambarin jam’iyyar da ke cikin takardar zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

“Kalubalan tantance tambarin jam’iyyata ga wadanda suka zabe ni da wadanda suka yi niyyar zaɓe na ya yi yawa. "Tambarin mu ya dishi-dishi, ko a zance na gaskiya ma a ce babu shi a cikin jerin jam'iyyu na kan takardar kaɗa ƙuri'a, wanda hakan ya rikitar da masu jefa min ƙuri'a," in ji ta.

 Mbakwe ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta buga tambarin jam'iyyar a kan takardun zabe. Ta ce hakan ya bata burinta da kuma kyakkyawar damar da take da shi na bayar da gudunmawar da ta dace wajen inganta Najeriya.

“Dukkanmu mun san cikakken bayanin tambarin NNPP, wanda shine ‘Kwandon ‘ya’yan itace’ da kuma sunan Jam’iyyar NNPP, yayin da INEC ba ta saka wani abu da yai kama da kwandon ‘ya’yan itatuwa da kuma sunan NNPP a takardar zabe.

"Tambarin NNPP da ke cikin takardar zabe ta INEC ya rikitar da yawancin magoya bayana kuma hakan ya sanya su ka wasu jam'iyyun kamar LP da YPP," in ji ta.


  #LABARAN SIYASA   #SAKAMAKON ZABE

Post a Comment

Previous Post Next Post