Ka zo Mu yi Tafiya Tare Don ci Gaban Kano - Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano ya yi kira ga Gawuna

Ka zo Mu yi Tafiya Tare Don ci Gaban Kano - Zaɓaɓɓen Gwamnan Kano ya yi kira ga Gawuna

 



Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya yi kira ga ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna da sauran ƴan takara da su zo a hada kai domin ciyar da Kano gaba.

Yusuf, wanda ake wa laƙabi da Abba Gida-Gida, ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi shaidar lashe zabe a yau Laraba a ofishin INEC a jihar Kano. A cewar Abba, tunda Gawuna ya riga ya fada a gurare da dama cewa zai karɓi duk abinda Allah Ya kaddara masa a zaɓen, to lokaci ya yi na ya rungumi ƙaddara ya kuma bada gudummawa a ciyar da jihar gaba.

“Mun samu labarin Gawuna ya sanar da kafafen watsa labarai kafin bayyana sakamakon zabe cewa idan bai yi nasara ba, zai karbi abin da Allah Ya kaddara. Don haka muna kira a gare shi da ya fito ya ja hankalin mutanensa su yarda da cewar wannan yin Allah ne,” in ji shi.

Ya ja hankalinsu da su yi koyi da jagoran jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya fadi zabe a 2003 amma ya taya wanda ya lashe zaben murna. Abba ya kuma yi alkawarin cewar matansa da ’ya’yansa ba za su samu wani mukamin da zai ba su damar shiga sharafin gwamnatinsa ba.

Yusuf, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan karbar takardar shaidar lashe zaben Gwamna a ofishin INEC da ke jihar, ya bayyana hakan ne kan yadda ake zargin iyalan gwamna Abdullahi Umar Ganduje suka yi tasiri wajen tafiyar da gwamnatin jihar.


Zababben gwamnan ya ce ba zai bai wa iyalansa damar shiga gwamnatinsa ba saboda ba tare aka rantsar da su ba domin yi ea al’ummar Jihar Kano aiki ba. “Matana ba za su kasance a gwamnati ba. ’Ya’yana ba za su kasance a cikin gwamnati ba. Kuma ina tabbatar muku da cewa mataimakina ma hakan ce za ta kasance,” a cewarsa.

Da yake magana game da gudunmawar jami’an tsaro a lokacin zaben gwamna a jihar, Abba ya gargadi jami’an tsaron da suka hada kai da jam’iyya mai mulki da su guji aikata hakan a gaba, inda ya bukace da su fifita hidimtawa ‘yan Najeriya ba tare da nuna wariya game da jam’iyya, Addini ko kuma kabilanci ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post