Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris INEC ta tabbatar wa da BBC ɗage zaɓen, bayan wani taron sirri da manyan jami'an hukumar suka yi a Abuja.
Kafofin yaÉ—a labarai na Najeriya sun ambato cewa INEC ba ta kammala saita na’urar tantance masu zaÉ“e ba ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaÉ“en shugaban Æ™asa a ranar 25 ga watan Fabirairu.
Sun Æ™ara da cewa hukumar ta ce sai ta samu damar kwashe bayananta da ta tattara na a yayin zaÉ“en shugaban Æ™asar zuwa wani rumbunta na daban kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi zaÉ“en gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba. Tun da farko, an tsara gudanar da zaÉ“en ne a ranar asabar 11 ga watan Maris.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kaÉ—an bayan wata kotun É—aukaka Æ™ara a Najeriya ta amince da buÆ™atar hukumar zaÉ“e ta Æ™asar ta sake saita na’urar tantance masu zaÉ“e ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaÉ“en shugaban Æ™asar.
Tawagar alƙalan kotun mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin Joseph Ikyegh ta yanke hukuncin cewa an bai wa INEC damar ne domin gudanar da zaɓen gwamnoni wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 11 ga watan Maris tun da fari.
Hukuncin na nufin kotun ta Æ™i amincewa da buÆ™atar da É—an takarar shugaban Æ™asa a jam’iyyar LP Peter Obi ya shigar ta neman hana INEC goge bayanan masu zaÉ“en da aka naÉ—a a zaÉ“en shugaban Æ™asar.
Tawagar alƙalan ta ce INEC ta bayyana cewa tana da shirin kwashe bayannan da ke cikin na'urar 176,000 da aka yi amfani da su a zaɓen ta wallafa su a wani rumbun bayananta na daban, ko da yake Obi da LP ba su nuna ƙin amincewa da wannan shiri ba.