Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, a yau Litinin ta tabbatar da cewa gobara ta kone wasu shaguna, wadanda ba ginannu ba, da kuma babban ginin tsohon bankin Savannah da ke kasuwar Singa a Kano. Sanarwar da kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ya fitar ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 02:18 na dare.
Mun samu kiran gaggawa da tsakar dare da misalin karfe 02:18 na dare daga wani Sai’du Hamza, cewa gobara ta tashi a kasuwar da ke karamar hukumar Fagge a jihar. Da samun labarin, mun yi gaggawar aika wasu jami’an mu da motar kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 02:22 na dare domin kashe gobarar da kuma dakile ta kada ta shafi sauran shaguna,” inji shi.
Sai dai Abdullahi ya ce gobarar ta kone shagunan da dama, inda ya kara da cewa har yanzu hukumar ba ta ganomusabbabin faruwar lamarin da kuma adadin shagunan da su ka ƙone