A Ranar Laraba 1 ga watan Maris, 2023, dakin sa idon mu ya karbi kiran gaggawa da misalin 5:23 na asuba daga wani Aliyu Alkasim. Ya bada rahoton barkewar gobara a kasuwar Kurmi, da ke karamar hukumar Birnin Kano''
Abdullahi ya ce a take bayan karbar rahoton, hukumar ta tura jami'an ta wajen da abin ya shafa. ''Mun tuntubi jami'an mu daga ofisoshin da ke kwaryar birni.
Da isar su wajen da misalin 5:27 na asuba, inda gobarar ya shafa ya kai kafa 160 X 100.'' Ya ce da kokarin jami'an su, hukumar tayi nasarar tseratar da shagunan kasuwar da dama kuma babu wanda yaji rauni ko ya rasa ransa.
Ya ce har yanzu ana binciken musabbabin gobarar. Ya kuma bukaci al'umma da su dinga kashe kayan amfanin lantarki da kuma datse hanyoyin lantarkin idan ba a amfani da su a kuma guji amfani da wuta a cikin kasuwa, Kimanin Shaguna 80 ne suka kone.