Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai tabbatar da sake fasalin Najeriya cikin watanni shida na mulkinsa idan an zabe shi, Ya bayyana haka ne a babban taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.
Abubakar, wanda ya samu wakilcin tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Okwesilieze Nwodo, ya ce an kammala isassun ayyukan bincike da ake bukata domin sake fasslin Najeriya.
Nwodo shi ne mataimakin darakta, bincike da dabaru, na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, PCC. Ya ce Najeriya za ta samu daidaito ne idan kowane yanki ya mallaki albarkatun kasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya tuna cewa ana kafa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki lokacin da yankuna ke sarrafa albarkatun su. Lokacin da muke magana game da sake fasalin tsarin mulki, a cikin watanni shida na farko, da kasar nan ba za ta zama abin da kuke gani a yau ba.
"An yi aiki da wannan kuma ina jira kawai a rantsar da ni a ranar 29 ga Mayu kuma za a fitar da tsare-tsaren." Inji shi.