Ringim wani yanki ne kuma karamar hukuma a jihar jigawa wadda take da helkwata acikin garin Ringim, tana da fadin kasa dayakai kilometer 1,057 kuma take da yawan mutane akalla mutum 320,552 a kiyasin da akai shekarar 2020. Tayi iyaka da garki a arewa, taura daga gabas, jahun daga kudu maso gabas, dutse daga kudu, ajingi daga kudu maso yamma, sai gabasawa daga yamma.
A shekarar alif 1930 akasamu primary ta farko Wato katutu primary school, inda aka Fara koyarwa mutum 39 a shekarar. Sannan daga baya aka kara samun wata primary mai suna sabon gida primary school a shekarar 1954 ankafa ta sakamakon shirin UPE. A shekarar 1976 angina wasu makarantu irinsu galadanchi primary school da kuma makarantar gwamnati ta secondary Wato ( government unity secondary school) inda ta shafe shekara 2 biyu wucin gadi a dawakin kudu dake jihar Kano.
Kafin ta Fara aikin koyarwa ta a Ringim, sannan itace makarantar secondary ta 3 UKU a Nigeria wadda take da yawan dalibai, wadda Kodaga wacce jiha ana kawo dalibai a fadin nijeriya. Makarantar .makarantar galadanchi primary school, makarantar St Peter school inda ta koma sabon gari primary school
Sannan Makaranta government day secondary school Ringim1994 dakuma bording primary school 2001. Ansamu Karin makarantu daga baya, Abdullahi mai masallaci Islamic secondary School Ringim, government secondary galadanchi Ringim, government girls secondary school Rinim, government day secondary school Arewa Ringim, government junior Arabic secondary school Ringim, government technical secondary School Ringim Da sauransu
Ansamu makarantar kwalejin koyarda ilmin sharia a shekarar alif 1991 bayan kirkirar sabuwar jihar jigawa da aka samu (college of education and legal studies).
Masarautar Ringim
Ankirkiro masarautar a shekarar alif 1991 bayan kirkiro jihar jigawa da akai zamanin Mulkin soji karkashin janar Ibrahim badamasi babangida, Alhaji Dr sayyadi Mahmud shine Sarkin yanka na farko a masarautar ta Ringim, masarautar Hada da kananan hukumomi 4 Ringim, Taura,Garki da Babura wanda kowannensu akwai gundumomin hakimai 4 cikin su dakuma dagatai kusan 12 kowanne.
Karfin tattalin arziki
Ringim kasa ce wacce ta shahara wajen noman gyada tun zamanin shekarun baya , kuma kasa mai kyan yanayi wajen noman, gero, ridi, tumatur, barkono, dawa, rogo, alkama, shinkafa, masara, tantasai da sauransu. Garin ya shahara wajen noman gyada tun zamanin turawan birtaniya inda suka gina titin jirgi (railway) tundaga jihar Kano, zuwa Ringim ta wuce Nguru ta jihar yobe.
Ringim tana da Albarkachin kayan marmari irinsu, goba, mangwaro, cashew, kankana, yalo, karas, dsss, mafi yawacin Mutanen gari karfin tattalin arzikinsu shine noma dakuma kasuwanci.