Takaitaccen Tarihin Hajiya Zulai Bebeji Jaruma kuma Uwa a Masana'antar Kannywood

Takaitaccen Tarihin Hajiya Zulai Bebeji Jaruma kuma Uwa a Masana'antar Kannywood



Da farko cikakken sunan Jarumar Shine Zulaihat Abdullahi Aliyu Bebeji, An haife ta a Karamar hukumar bebeji dake jihar kano. Ta girma a Gawuna dake karamar hukumar nassarawa, a hanun yayar mahaifiyarta hajiya Harira da mijinta mallam Ladan.


Ta fara karatun Boko da Islamiyya a Unguwar gawuna. Daga bisani bayan tayi aure a taci gaba da karatu, bayan nan kuma ta shiga masana'antar kannywood inda take fitowa a matsayin uwa a cikin fina finan da takeyi, hajiya zulai ta shafe shekaru da dama acikin wannan masana'anta.


Kalli Cikakken Bidiyon 👇




Allah yayiwa mahaifan Hajiya Zulai Rasuwa, Mahaifinta Mai Suna Alhaji Abdullahi Aliyu Da Mahaifiyar ta Malama Salamatu Sulaiman Muhammad Abdullahi Maje Karofi Ubangiji Allah yayi musu Rahama.




Hajiya Zulai ta haifi 'ya'ya Shida guda biyu sun Rasu hudu suna Raye Wadanda Suka Rasu sune Usman wanda ake wa lakabi da Halifa da Fatimatu Zara'u wadda akewa lakabi da Hajjaju, Allah yayi musu Rahama A yanzu hajiya na da 'ya'ya hudu da kuma jikoki da dama.






           #LABARAI           #KUNDIN TARIHI


Post a Comment

Previous Post Next Post