Hukumar Zaɓe Maizaman kanta ta Ƙasa, INEC, ta ayyana Sanata Barau Jibrin na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan Kano-ta-Arewa. Jami'in tattara sakamakon zaɓe na yankin, Farfesa Tijjani Magaji Bamanga shi ne ya bayyana zaɓen a jiya lahadi.
Sanata Barau ya samu kuri’u 234, 652 wanda hakan ya sa ya samu nasara a kan babban abokin karawar sa na jam’iyyar NNPP, Dakta Baffa Bichi, wanda ya samu kuri’u 177, 014.
Sai dai ka kafin bayyana sakamakon zaɓen, sai da wakilin jam’iyyar NNPP ya bukaci jami’in zaben da ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda zargin cewa adadin wadanda su ka kaɗa kuri’a sun fi na wadanda aka tantance yawa.
Sai dai jami’in zaben ya bayyana masa cewa babu isassun shaidu a kan hakan, inda ya bukace shi ya kai rahoton duk wani korafi ga INEC ko kotu.