An Kama Ciyamomin Kananan Hukumomi Biyu da Bindigu a Kano

An Kama Ciyamomin Kananan Hukumomi Biyu da Bindigu a Kano

 



Rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ta hada da sojoji, Æ´ansanda, SSS da NSCDC, sun kama shugabannin kananan hukumomin Ungogo da Rimingado na jihar Kano, Abdullahi Ramat da Munir Dahiru da bindigu.

Wata majiyar sirri ta jami'an tsaro ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa an kama mutanen biyu ne a lokacin da su ke jagorantar Æ´an daba domin su kai farmaki kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, a hanyar Zariya, Kano.

Rundunar tsaron ta hadin guiwa na tsaka da sintiri na tauna tsakuwa a lokacin da su ka ci karo da shugabannin da ke jagorantar ‘yan daba. Nan take jami’an tsaro su ka karÉ“e bindigogin daga hannun ciyamomin tare da cafke ‘yan baranda sama da 100 da suka yi wa dan takarar jam’iyyar NNPP kwanton bauna.

Majiyar ta kara da cewa, "A halin yanzu ana tsare da su a sashin binciken manyan laifuka, kuma jami'an tsaro na hadin gwiwa na ci gaba da sintiri a cikin birnin domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin."

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano Abdullahi Kiyawa bai amsa kiran da DAILY NIGERIAN ta yi masa da sakon kar ta kwana ba har zuwa lokacin hada rahoton.


        #LABARAI                  #SIYASA

Post a Comment

Previous Post Next Post