Hukumar Kwalejin Shari’a da ilimin addinin musulunci ta Malam Aminu Kano wato Legal, tana sanar da dalibai, iyaye da daukacin al’umma cewar, zata fara sayar da fom din ta na zangon karatun shekarar 2022/2023 a dukkanin kwasa-kwasan kwalejin na matakin karatun Diploma da kuma NCE regular da part time.
Za'a fara sayar da fom din ne a ranar Litinin 13 ga watan fabrairu shekarar dubu biyu da ashirin da uku (2023) 13/02/2023. Domin haka,an bude shafin internet na kwalejin wato, www.akcils.edu.ng domin fara regista kai tsaye. Wadanda basu zabi Kwalejin Legal ba tun da farko su ziyarci ofishin JAMB domin su sauya zabin na su.
Sanarwa ta fito daga:
Dr. Salisu Marafa Sagagi jami'in hulda da jama’a na kwalejin a madadin Magatakarda.
Tags:
Admission