Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ta gudanar da taron yaye ɗalibai karo na 36 da na 37 a haɗe a yau Talata, inda dalibai 285 su ka kammala karatun digiri da sakamako mafi girma. Shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas ne ya bayyana a wajen bikin, ya na mai cewa dalibai 2,807 ne a ka yaye a zangon karatu na 2018/2019, yayin da 2,841 suka sauke karatu a 2019/2020 a tsangayun jami’ar 16.
Ya ce dalibai 8,777 da su ka kammala karatun digiri ne da suka kunshi 3,671 na 2018/2019 da kuma 5,106 na 2019/2020 sun fito daga Makarantar Digiri na biyu da kuma Makarantar Kasuwanci ta Dangote. Ya kara da cewa dalibai 359 da su ka kammala karatun digiri za su samu sakamakon digiri na uku; 5,936 za su sami Digiri na biyu, yayin da za a ba da Diplomas ɗin Difloma ga 'yan takara 2,484.
Abbas ya ce jami'ar na da dalilai masu kyau na yin bikin yaye daliban duba da irin nasarorin da ta samu. A cewarsa, jami'ar babbar jami'a ce a duniya da ke da himma ga ilimi, bincike da ayyukan al'umma a karni na 21.