Wasu Yan Najeriya Sun Koma Amfani da CFA a Maimakon Naira

Wasu Yan Najeriya Sun Koma Amfani da CFA a Maimakon Naira



Rahotanni daga jihar Sokoto na nuna cewar wasu mutane sun fara amfani da kudin CFA a maimakon Naira a wurin gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum, Bayannai sun nuna cewar akasarin masu cinikayya da kudin CFA masu mu’amalla ne da ‘yan kasuwa masu zuwa daga Jamhuriyar Nijar.

Tun dai bayan da aka fara samun matsalolin cire sabbin kudin Naira ne wasu ‘yan kasuwa musamman masu gudanar da harkokin kasuwanci tsakaninsu da ‘yan Nijar suka koma amfani da kudin na CFA kasantuwar babu manyan kudin Naira, Alhaji Rila dan kasuwa ne a tsohuwar kasuwar Sokoto, ya kuma ce sababbin dabaru ne ke fitowa a hankali domin samun mafita, yayin da darajar CFA ta rikito saboda sabon salon da aka bullo da shi.


Shi ma dai Junaidu ya ce, akwai hanyoyin da ‘yan kasuwar kan bi wajen biya wa kansu bukatar gudanar da harkokin cinikayya ba tare da sun dogara kacokan ga Naira Najeriya ba, lura da yadda kullum ta kasance dole a yi kasuwancin tsakanin ‘yan Najeriya da Nijar a tsohuwar kasuwar Sokoto, Labarin haka yake a wurin masu kasuwancin wayar salula da suka bayyana cewar, wani zubin akan bada kudin Naira, idan ba su isa ba, sai a cike ragowar da kudin CFA.


       #FARASHIN CFA          #LABARAI      

Post a Comment

Previous Post Next Post