Wasu Daga cikin Amfanin Beran Computer Wanda Ba Kowane Yasan Su Ba | Computer Mouse

Wasu Daga cikin Amfanin Beran Computer Wanda Ba Kowane Yasan Su Ba | Computer Mouse


Mouse kamar yadda kuka sani shi ne ake cewa dan beran Na'ura mai kwakwalwa ya kasance misali na input devices, shi ne wadda ya motsa kibiya ko kuso dake cikin na'ura mai kwakwalwa, yana da madannu guda biyu madannar hagu da kuma dama (Right and Left Click) sannan akwai taya (tyre) a tsakaninsu.

Madannar Dama (Right click) ana amfani da ita ne wajen bude menu acikin folder ko kuma filin monitor na na'ura mai kwakwalwa, Madannar Hagu (Left click) ana amfani dashi wajen zabar Abun ko budeshi a na'ura mai kwakwalwa. Budewa zaka danna shi sau biyu zai bude abunda kakeson budewa, inka danna sau daya kuma zai zabi abinda kakeso.


Taya (Scroll wheel, or ball or tyre) ana amfani da itane wajen nemo wani Abu dake sama ko kasa idan anbude folder ko word document ko wani Abu Wanda ana iya zuwa sama da kasa.


      #TECHNOLOGY                #TRICKS

Post a Comment

Previous Post Next Post