Waiwaye: Yau Shekara Daya Cif Da Rasuwar Sheikh Ahmad Bamba

Waiwaye: Yau Shekara Daya Cif Da Rasuwar Sheikh Ahmad Bamba



Labarin rasuwar malamin Musulunci, Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Bamba, a ranar 7 ga watan janairun 2022 ta girgiza mutane, daga mai istirja’i, sai mai hailala, sai mai zubar da hawaye, sai mai salati, sai mai yi masa addu’a. rana ce da hantar al’ummar Musulumi ta kada, musamman daliban ilimi a Najeriya da sauran wurare.

Sheikh Dokta Ahmad Bamba, wanda Allah Ya yi wa rasuwa sakamakon jinya, tsohon malami ne a Jami’ar Madina da ke Saudiyya, inda ya shafe sama da shekara 20 yana daukar darasi a Masallacin Annabi Muhammad (S.A.W) da ke Madina.

Sannan kuma tsohon malami ne a Jami’ar Bayero ta Kano, bayan nan ya shafe kimanin shekaru 40 yana jagorantar majalisin ilimi a Kano kuma karatuttukansa sun bazu a duniya cikin harshen Hausa.

A majalisin nasa, ya fassara manyan litattafan Musulunci irin su, Muwadda Mali da Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunanu Abi Dawud da Sunanu Nasa’i da Sunanu Tirmizi da Sunanu Ibn Maja da Sunanu Darimi da Musnad Ahmad bn Hambal da sauransu.

Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Bamba, wanda aka fi sani da Dokta Ahmad BUK ko Ahmad Bamba, tun yana raye al’umma ke masa kyakkyawar shaida game da kyawun dabi’unsa da tsantseninsa da kuma nisantar harkokin siyasa.

Malami ne kuma ga manyan malaman Musulunci da suka yi fice a duniya, ciki har da marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam kuma ya kasance abin koyi ga daliban ilimi da sauran mutane, a Kano da sauran wurare.

Ya fara assasa majalisinsa na Darul Hadis ne a Masallacin Juma’a da ke tsohuwar harabar Jami’ar Bayero, kafin daga baya ya koma masallacinsa da ke Tudun Yola.

Post a Comment

Previous Post Next Post