Wata mata mai suna Malama Khadija, a yankin Karamar Hukumar Rano da ke jihar Kano, ta kashe aurenta sannan kuma ta auri saurayin ’yarta, Lamarin ya faru ne bayan ’yar tata mai suna A’isha, ta ki amincewa da saurayin da ya zo neman aurenta, inda ita kuwa uwar ta ce ta ji ta gani, tun da dai Musulunci bai hana ba.
Tun da farko dai, ’yan uwan matar sun shaida wa gidan rediyon Freedom cewa suna zargin Kwamandan Hukumar Hizbah a Karamar Hukumar da aurar da ’yarsu ba tare da amincewarsu ba, inda suka ce ba su ma san inda take ba.To amma Khadija ta ce lafiyarta kalau, kuma tana zaune lafiya da sabon angonta.
Ta ce bayan ta gano ’yarta ba ta son mutumin, sai ta ce bai kamata duka su taru su yi asarar shi ba, inda ta tuntubi iyalinsa, inda ta ce ita ma kyakkyawa ce kamar diyar tata. Khadija ta kuma ce, “Ba a jahilce na aikata haka ba. Sai da na tambayi malamai kuma suka tabbatar min da halaccin yin haka.
“Da na tambaye shi sai ya amince, amma iyayena da ’yan uwana suka ki daura auren. Dalilin ke nan da na yanke shawarar zuwa Hizbah, yanzu ga shi har mun yi aurenmu lafiya,” in ji ta.
Wani Kawun Khadija mai suna Abdullahi Musa Rano, ya ce da gangan suka ki amince mata ta auri sabon mijin tun da farko saboda suna zargin da gangan ta kashe aurenta na farko domin ta auri saurayin ’yar tata. Ya ce, “Ta matsa wa tsohon mijinta lamba kan ya sake ta saboda ta auri wancan. Mu kuma muka ce ba za a yi wannan abin kunyar a danginmu ba, shi ya sa muka ki amincewa da bikin.
“Ba ma farin ciki da abin da Hizbah ta yi, kuma muna bayyana shi ne saboda mu kwato ’yarmu, muna so Babban Kwamandan Hizbah da Gwamnatin Jiha su saka baki a ciki,” in ji shi. Sai dai da aka tuntubi Kwamandan na Hizbah a Karamar Hukumar, Ustaz Nura Rano, ya ce hedkwatar hukumar ta Jiha ce kawai take da hurumin yin magana a kan lamarin.
Shi ma da aka tuntube shi, Babban Kwamandan Hizbah na Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, ya yi alkawarin bincika lamarin.