kankiya Gari ne da aka kafa shi tun lokacin mulkin Habe. Kamar kowane gari na kasar Hausa itama kankiyar tanada nata Tarihin. Labarin ya nuna mana cewa, kankiya gari ne mai hadarin gaske domin rukukin daji ne gun, wannan Dalilin ne yasa mazauna wurin suka rika gudu suna barin garin.
A cikin Irin wadan nan dabbobin a kwai wani naman Dawa da ya addabi mazauna gurin harma da su Kansu dabbobin. Mazauna gurin sunyi iyakar yinsu Dan su kashe wannan dabba mai suna KANKI. Kankin nan ya gagara har saida wani mafarauci da ake kira da suna YA.
Also Read: Taƙaitaccen Sharhi Akan Littafin Tafiya Mabuɗin Ilmi Na Alhaji Abubakar Imam
• Takaitaccen Tarihin Kofar Marusa Dake Jihar Katsina
An ce Ya din yaje dajin shi daya ya kashe wannan dabba wadda ake cema kanki ya kawo Gida ya aje. Da labari ya bazu cewa wannan mutum mai suna YA ya kashe kanki sai aka rika zuwa gidan shi domin mutane su ganewa idon su, daga nan ne mutane idan za suje gidan sai su rika cewa " Bari muje gidan YA muga KANKI, sai mutane suce wane kanki sai ace kanki ya.
yau da gobe sunan sai ya zama kankiya. Amma a wani labarin an nuna mana cewa, wani Buzu yazo, da yazo sai ya sauka inda yanzu ake kira da kankiya yazo daga Agadaz. Ya zauna a rukunin dajin dake gurin, sunan wannan Buzu KIYA a inda ya rika sayen abubuwa daga mazauna gurin kamar Irin su hatsi da tabarmi da bayi da dai sauransu, yana saida wa bakin dake zuwa nan da kuma wayanda ke kan hanyar wucewa zuwa kano.
Sai kuma ya sayi abubuwa da fataken suka kawo kamar su tufafin sawa da Dabino da gishiri da sauransu. Yau da Gobe sai karayar arziki ta zo mashi, ya talauce, ya rasa duk abinda ya mallaka. Dadin dadawa sai matar shi wacce yakeji da ita ta kwanta ta mutu. Wannan shi yasa KIYA ya rude, ya shiga daji yana yiwa fataken da suke wucewa zuwa kano fashi. Nan da nan kiya ya zama shahararren Dan Fashi, musamman da suka hadu da wasu yan fashin suna fashin tare.
Da labarin wannan Dan fashin ya isa gun Sarkin Katsina na wancan lokacin sai aka turo da mayaka daga Katsina aka je aka fasa tawagar Barayin, shi kuma KIYA aka kashe shi, aka yanke kansa aka kaiwa Sarkin Katsina don ya gani. Da Sarki ya gani sai yayi umurni da aje a rataye kan a daidai inda Fataken ke bi don su gani su tabbatar da cewa an kashe kiya din. To, daga nan ne sai aka ce, " kaga kan kiya "?
Ko kuma a ce " za mu je mu ga kan kiya", Wanda daga nan ne Kalmar kankiya ta ginu da har ya zuwa yau da muke Ciki a wannan zamani. A wani bayanin da muka samu an nuna cewa, wani mutum mai suna Gunguna shi ne mutum na farko daya fara zama a gurin da yanzu ake cema kankiya. A lokacin kuwa daji ne so sai gurin.
Da mutane suka zo daga baya suka zauna, sai suka Nada Gunguna ya zama shugaban su ko kuma Sarkin dake gurin. Abdullahi Mohammed wani masanin Tarihi ya nuna cewa, al'umma da yawa daga wurare daban daban sun zo kankiya sun zauna. A kwai kanawa da ake kyautata sun zo gun tun wajen karni na 15, suka zauna a arewacin kankiya, a wurin da yanzu ake kira da Unguwar kanawa.
Haka kuma, wadansu Maguzawa sun zo wadanda suka kafa mazauninsu a kudancin kankiya, a wurin da yanzu ake kira Zango. Har ila yau, a daidai wannan lokacin wasu Maguzawan sun zo sun kafa tasu unguwar a inda yanzu ake kira da Sabon-Layi. Saboda kasancewar duk wadannan mazauna gurin mafarauta ne sai suka hada Kansu a karkashin mulkin Gunguna da aka ambata a baya. Haka suka cigaba da zaman su in wannan ya mutu sai wannan ya gaji Mulkin har zuwa lokacin da jihadi ya bayyana na Shehu Usman bin Fodio.